Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, yana da ministoci 110 wanda hakan ya mayar da gwamnatinsa mafi yawan ministoci a tarihin Ghana. Sai dai duk da yake shugaban ya yiwa mukarraban na sa garambawul, amma ‘yan adawa na ganin hakan ba zai kawo ci gaba ba a kasar kasancewar yawansu babu abin da zai harfar sai ‘kara barnata kudin gwamnati.
Yanzu haka dai baki daya ministocin da aka sauyawa wuraren aiki zasu fuskanci tantancewa daga Majalisar Dokokin Ghana, kafin a tabbatar musu da mukamansu.
Cikin manyan sauye-sauyen da aka yi akwai John Peter Amewu, dake zama tsohon ministan filaye da alabarkatun kasa, wanda yanzu haka aka mayar da shi ministan makamashi. Shi dai Mista Amewu, yayi kaurin suna a yaki da masu hakar zinari ta barauniyar hanya a kasar Ghana.
Sai kuma ministan yada labarai, Dakta Mustapha Abdulhamid, da yanzu haka aka mayar da shi ministan raya birane da zango. Shi kuma tsohon ministan Zango Boniface Abubakar Saddique, ya zamanto ministan ‘kasa a ofishin mataimakin shugaban ‘kasa.
Haka zalika ita kuma ministar kare mata da yara, yanzu haka ta zama sabuwar jakadiyar Ghana a kasar Italiya.
Sai dai ‘yan adawa na ganin shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, baya ji ko kula da kukan ‘yan ‘kasarsa dake cewa a duba a gyara yawan ministocin da ake da su.
Domin karin bayani saurari rahotan Ridwan Abbas.
Facebook Forum