Kasa da mako biyu gabanin rufe raba katin zaben shekarar 2019, an samu karuwar mutane dake dafifi a wuraren yin rajistan samun katin.
Sashen Hausa ya zagaya wasu wuraren domin ganin abubuwan dake faruwa.
Malama Zainab Aliyu, da ta samu ta yi rajista ta ce yanzu da zara ranar zabe ta zo ba sai ta je ta bi wani dogon layi ba. Za ta je gaba gadi ta jefa kuri'arta cikin ruwan sanyi. Shi ma Sani Muhammad Awal, ya ce ya yi rajista ya kuma samu kati. Shi kam ya taba yin katin zabe a lokacin gwamnatin Obasanjo. A cewarsa ya yi katin ne saboda ya zabi abun da ya ke zato zai kawowa kasarsa ci gaba.
Kawo yanzu a wajejen Abujan, kimanin mutane miliyan 11 suka mallaki katin zaben, tun daga lokacin da hukumar zabe ta fara yiwa 'yan kasa rajista a watan Afirilun bara.
Kakakin hukumar INEC a Abuja Aliyu Bello, yana cewa tun daga watan Afirilu zuwa karshen bara, an yiwa mutane miliyan uku da rabi rajista, amma daga watan Janairun wannan shekara zuwa yanzu, an yiwa mutane fiye da miliyan bakwai da rabi rajista. A cewarsa hukumar zaben ta fitar da shirin ne domin baiwa kowane dan Nigeria damar jefa kuri'a lokacin zabe mai zuwa.
To sai dai duk da tururuwar da wasu ke yi na tabbatar sun yi rajista sun kuma samu katin zabe, wasu suna nuna halin "ko in kula". Wani mai suna Abubakar, ya ce shi bai yi rajista ba saboda bin dogon layi da cin lokaci. Ya kara da cewa ko ya yi rajistan ma ba za'a samu wani sakamako mai kyau ba.Kazalika Habiba Yakubu lokacin da ta bata can farko domin samun katin ya sa yanzu ma ba ta nuna sha'awar neman ta samu ba.
A saurari rahoton Hauwa Umar domin karin bayani
Facebook Forum