Ranar 29 ga wannan watan Mayu ne gwamnatin Shugaba Buhari zata cika shekara biyu da kama mulkin Najeriya.
Kakakin shugaban Najeriya Garba Shehu yace nasarorin da shugaban ya samu sun hada da sako wasu cikin 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace a shekarar 2014 daga makarantarsu.
Kazalika jama'a suna ganin yadda zaman lafiya yake dawowa a karkashin shugabanci Muhammad Buhari. Garba Shehu yace baicin nasarar da dakarun gwamnati ke samu akan 'yan ta'adan Boko Haram da tsagerun Niger Delta ta kuma bude wata kafar tattaunawa domin samun sulhu.
Dangane da batun 'yan matan Chibok Malam Garba Shehu yace hanyar tattaunawa da 'yan ta'adan ya kaiga sako fiye da rabin 'yan matan da aka sace. Haka ma an samu sako yara da mata da aka sace fiye da dubu goma sha biyu.
Mai goyawa Shugaba Buhari baya Salihu Isa Nataro Kebbi yace shugaba Buhari ya ba mara da kunya musamman ta fuskar farfado da mutuncin Najeriya a idanun duniya
To saidai manyan 'yan adawa irinsu tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa sun yi shagube da batun nasarar gwamnatin APC a karkashin Buhari.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5