Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Sanin Yakamata Ne Kiran Buhari Yayi Murabus: Doyin Okupe


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaban PDP na arewa maso yama yace zasu kada Muhammadu Buhari warwas Allah ya bashi lafiya a buga

Tsohon mai taimakawa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ta fannin hulda da jama’a Doyin Okupe, yace rashin sanin yakamata ne kira da wasu keyi cewa shugaba Muhammadu Buhari, yayi murabus domin jinya da ta same shi.

Okupe, a wata sanarwa yace rashin lafiya da mutuwa na kan kowa don haka kira ga shugaban yayi murabus sam ba matsaya ce na tunani ba.

Doyin Okupe wanda ya kasance baya marawa Buhari baya amma batun kira da yayi murabus abun takaici ne, a matsayinsa na wanda ya fito daga yankin kudu yace tundawowar dimokradiya 1999, kudu tayi mulki na tsawon shekaru goma sha hudu (14) inda arewa ta sami hudu (4) don haka yake da ra’ayin a 2019, mulkin ya sake zama a yankin arewa maso yamma.

Shugaban PDP, na arewa maso yamma Ibrahim Kazaure, yayi alwashin cewa koda Buhari, adawa zata yi takara ta gaba PDP, zata samu nasara.

Ya kara da cewa Allah ya baiwa shugaba Buhari lafiya ya zo PDP, ta kada shi warwas domin a cewarsa PDP, bata so ta karbi mulki a hannun wani taga taga sai a hannun wanda ake ji dashi watau Muhammadu Buhari

Shugabanin addini irin su Sheikh Tijjani Bala Kala Rawi, na kiran ‘yan siyasa da su rika yin taka tsan tsan kam lamuran mulki da dimokradiya.

Koma mai za a ce an ga mulki salo hudu a Najereiya, na mulkin mallaka Sojoji da fararen hula da suka dade kan mulki inda adawa tayi kukan kura ta amshi madafun iko.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:05 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG