Wakilan VOA sun isa birnin N’Djamena don kawo rahottani akan yarejejniyar tsagaita wuta tsakanin Boko Haram da Gwamnatin Nigeria.
WASHINGTON, DC —
Daya daga cikin wakilan Sashen Hausa na VOA da yanzu haka suke a birnin N’Djamena, Mamadou Danda, wanda yayi tattaki daga kasar Kamaru zuwa kasar Chad don ganin wainar da ake toyawa dangane da kokarin shirya yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin gwamnatin Nigeria da ‘yan kungiyar Boko Haram, yace har yanzu, a zahiri, ba’a fara wannan taron ba. Amma yace yana magana ne bisa ga abinda ido ke gani don, a cewarsa, mai yiyuwa ne ana wata tattaunawar a can bayan fage da jama’a basa gani. Daga can N’Djamenna, ga rahoton na Mamadou Danda:
Your browser doesn’t support HTML5
Agogon Daliban Chibok
Yawan lokacinda ya wuce tun daga ranar da aka sace ‘yan matan Chibok.