Garuruwa a kalla 445 ne aka gano cewa sun fada cikin yanayin karancin abinci a jihar Tilabery bayan da al’umomi suka kauracewa gonaki bana, yayin da kasuwanni da dama suka daina ci sanadiyar kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yiwa fararen hula a gonakinsu, kokuma akan hanyar zuwa cin kasuwa.
A rahotan kungiyar agajin OCHA ta MDD ya ce mutane kusan 600,000 ne ke fuskantar wannan barazana ta karancin abinci. Dakta Modibo Traore shine shugaban reshen wannan kungiya a Nijer.
Ya ce an zo karshen damunar 2021 kasancewa wadanan al’umomi ba su yi noma baba makawa za a yi fama da yunwa a wasu sassan jihar Tilabery, kamar su Ouallam da Banibangou da Filingue har ma da Torodi da Say sakamakon matsalar tsaron da ta hana dubban mutane zuwa gonakinsu. Ya kamata a san cewa yanki ne da ke da ‘yan gudun hijirar cikin gida fiye da 100,000 baya ga dubban ‘yan Mali da ‘yan Burkina Faso dake hijira.
Karkarar Anzourou na daga cikin wuraren da aka yi fama da irin wannan tashin hankali da ya hana jama’a aiki a daji.
Gundumar Banibangou mai mabukata 79,000 na kan gaba a yawan wadanda wannan matsala ke shafa inji rahoton na OCHA. Wani dan rajin kare hakkin jama’a Mahamadou Haldi ya yi kira a dubi halin da al’umar yankin Tilabery ke ciki a kuma agaza musu.
Ba ya ga batun tabarbarewar tsaro kungiyar ta OCHA ta ce daukewar ruwan sama a wani lokacin da amfanin gonaki ke kokarin kosawa a damunar da ta gabatada illolin annobar coronavirus ta haifar na daga cikin dalilan da suka jefa jama’ar yankin Tilabery cikin wannan yanayi na yiyuwar fuskantar barazanar karancin abinci.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5