Matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na kafa kwamiti domin ya duba rage wasu ofisoshin jakadancin da Najeriya take da su a wasu kasashen waje, yana samun yabo daga wasu masana da 'yan Najeriya.
A farkon makon nan ne shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka lokacin da kwamitin manyan shugabannin ma'aikatar harkokin wajen Najeriya karkashin jagorancin babban sakataren ma'aikatar Ambasada Bulus Lolo, suka kai masa ziyara a fadar gwamnati dake Abuja.
Da yake magana shugaba Buhari, yace gaskiyar magana itace Najeriya bata da karfin ci gaba da daukar nauyin wadannan ofisoshi.
Da tofa albarkacin bakinsa, Ibrahim Dahiru Dan Jarida yace wannan mataki yana da kyau domin Najeriya bata bukatar wasu ofisoshin. Ya bada misali da kasar Saudiyya wacce bata da ofishin jakadanci a Ghana, jakadanta na Najeriya shi yake kula da kasar Ghana.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5