Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ghana Ya Tarbi Buhari


Ghana Ghana John Dramani Mahama
Ghana Ghana John Dramani Mahama

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a kasar Ghana inda zai kwashe yinin yau yana tattaunawa da takwaran aikinsa John Dramani Mahama.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Ghana domin kai ziyarar aiki ta wuni guda.

Buhari ya sauka a filin tashin jirage na Kotoka da misalin karfe 10 na safe agogon Ghana, inda aka karrama shi da ala'dar kewaya dakarun kasar.

Shugaba Buhari ya samu tarbar takwaran aikinsa, John Dramani Mahama, wanda zai gana da shi kan huldar kasuwanci da wasu batutuwa da dama.

Baya ga haka dumbin ‘yan Najeriya mazauna kasar suma sun tarbi shugaba Buhari wanda ke sanye da babbar riga.

Tuni rahotanni suka ce ashugabannin biyu sun fara tattaunawa a Fadar shugaban kasar Ghana ta Peduase.

Wasu ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan ziyara inda wasu suka nuna farin ciki yayin da wasu kuma suka nuna rashin gamsuwarsu kan wannan ziyara, kamar yadda za ku ji a sautin da ke kasan wannan rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG