Batutuwan tsaro da yaki da rashawa da yunkurin tayar da komadar tattalin arziki na daga cikin al’amuran da suka mamaye jawabin shugaba Mohammadu Buhari. Bayan ga bayyana murna game da yadda dakarun Najeriya suka kwato dajin Sambisa daga hannun mayakan Boko Haram.
Shugaba Buhari yace gwamnati na sane da kura-kuran da aka tafka game da zargin karkatar akalar kudaden tallafa ‘yan gudun hijira fiye da mutane Miliyan biyu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kuma ana daukar matakan ladabtar da masu hannu a kai.
Sai dai da alama lafazin na shugaba Buhari bai gamsar da kungiyoyin rajin tabbatar da adalci a shugabanci ba, Kwamarad Nura Ma’aji, wanda ke da shakku kan dai dai ta al’mura a Najeriya, ganin cewa Majalisar Dokoki ta samu sakataren gwamnatin tarayya da yin badakala, amma shugaba Buhari ya kira da sunan kuskure.
Shi kuma lauya Abdullahi Bulama Bukarci, shugaban kungiyar Arewa Concern Citizen, cewa yayi jawabin na shugaba Buhari yayi kama da na shekarar da ta gabata.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5