Inji Dr. Garba Abari 'yan Najeriya sun san inda suka fito sun kuma san inda suke a yau saboda abun da aka fada lokacin fafutikar zabe an cika.
Babban daraktan hukumar wayar da kawunan jama'a ta Najeriya ko NOA Dr. Garba Abari yana ganin gwamnatin APC da shugaba Buhari ke jagoranta ta cika alkawuran kemfen koda ma akwai abun da ya saura bai wuce nafila ba.
Inji daraktan, hukumarsa zata cigaba da karfafawa jama'a gwuiwa su fallasa miyagu da take-taken 'yan ta'ada. Ya kira mutane suyi la'akari da inda zasu je suyi kasuwanci. Su yi takatsantsan da duk wani abun da basu amince dashi ba su jawo hankalin hukuma. Watakila mutum ya ga wata 'yar jaka ko kwali ba'a san wanda ya ajiyeshi ba a sanarda jami'an tsaro.
Abubakar Abdulkadir Jamari dalibin jami'a ne yace ya amince da matsayin hukumar wayar da kawunan mutane ko NOA a takaice musamman ma da yake shi daga yankin arewa maso gabas ya fito, yankin da ya sha fama da ta'adancin 'yan Boko Haram. Yace bana sun ga canji sosai. An samu zaman lafiya ba kamar da ba.
Barrister Modibo Bakari lauya mai zaman kansa dake Abuja yana da ja a bangaren yaki da cin hanci. Yana ganin muddin gwamnatin Buhari bata kafa kotuna na musamman ba to ko ba za'a samu wani hukumci mai tasiri ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.