Garambawul ga tsarin musayar kudaden ketare da hana shigar da wasu kayayyaki cikin Najeriya, da kuma matakin rufe iyakokin ‘kasa na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta ‘dauka domin karfafa gwiwar kamfanonin kasar su bunkasa.
Babban jami’i a sabon kamfanin sarrafa Tumatiri na ‘Dangote dake Kadawa a jihar Kano, Mallam Jafar Sani Bello, yace duk da yake basa shigo da komai daga ketare gabanin su gudanar da ayyukansu, amma wasu daga cikin matakan da gwamnati ta ‘dauka na haifar da kaluble a gare su.
Mallam jafar, yace amfani da musayar kudaden ketare ya zama wajibi idan aka duba ga yadda kayayyaki sukayi tashin gwauron zabi, kamar Man da suke amfani da shi wajen samun hasken wutar lantarki da gyaran injinan da suke amfani da su wadanda aka kera a kasashen waje, hakan yasa da zarar kudin Dala ya tashi dole ne ya shafi al’amuransu.
Tuni dai kamfanin Erisco dake Legas, mai ayyukan sarrafa Tumatiri ya sanar da cewa zai komawa kasar China da Ghana domin ci gaba da gudanar da lamuransa saboda matsalolin musayar kudi da mahukuntan kamfanin suka ce suna fuskanta.
Haka zalika wasu kananan masana’antu sun koka da matakin sanya ababen adana Tumatiri a jerin kayayyakin da gwamnati ta haramta shigar da su Najeriya, lamarin da suka ce ka iya tilasta su su rufe aikace aikacensu nan da watanni uku masu zuwa.
Yanzu haka dai wasu manoma ma na bayyana irin kalubalen da suke fuskanta, Mallam Alfa Shitu, dake zaman manomin Tumatiri yace yanzu haka suna fuskantar matsalar tsadar Taki da maganin Feshi da kuma injin da suke amfani da shi a gonakinsu.
Domin karin bayani saurari rahoto na musamman daga Mahmud Ibrahim Kwari.