Ranar 21 ga watan Fabrariru, rana ce da ‘yan Jamhuriyar Nijar za su garzaya zuwa rumfunan zabe domin zaben shugaban kas ada na ‘yan majalisun dokoki.
WASHINGTON D.C. —
Wannan zabe dai ya ja hankulan mutane da dama a kasar ta Nijar da ma ketare, musamman idan aka la’akkari da yawan ‘yan takara shugaban kasa 15 da aka samu a wannan karo.
Daga cikin batutuwan da za su yi tasiri a wannan zabe a cewar kwararru a fannin siyasa akwai batun tsare dan adawa kuma tsohon shugaban Majalisa Hama Amadu da hukumomin kasar suka yi.
Baya ga haka akwai batun yadda ake tafiyar tattalin arzikin kasar wanda dukkanin ‘yan takarar su ka sha alwashin bunkasawa.
Saurari ra’ayoyin ‘yan Nijar mazauna birnin Konni kan yadda su ke kallon wannan zabe da ke tafe a tattaunawarsu da Ibrahim Ka’Almasih Garba:
Your browser doesn’t support HTML5