Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin wake rike da tattalin arzikin Nijar?


Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou kuma daya daga cikin 'yan takara
Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou kuma daya daga cikin 'yan takara

A yayin da kasar Nijar ke shirin zaben shugaban kasa da 'yan majalisu 'yan kasan na korafin rashin cin gajiyar anfani albarkatun kasa da Allah ya yi masu to ko me ya kawo hakan? Akwai bayani.

A daidai lokacin da zaben shugaban kasar Nijar ke cigaba da karatowa, 'yan siyasa masu neman shugabancin kasar na cigaba da bayyana manufofinsu tare da hobasan da zasu yi domin habaka tattalin arzikin kasar.

Amma hankalin 'yan kasar ya fi karkata ne kan batun tattalin arzikinkasar da yadda za'a dama dasu kamar kwatankwacin abun da suke gani a wasu kasashe.

Kasar Nijar dai ta mallaki ma'adanai da dama kaman karfen uranium dan man fetur da zinariya da gawayi da dai sauransu. Amma duk da wadannan abubuwa da ta mallaka kasar tana cikin kasashen da suka fi talauci a duniya. Alkalumma sun nuna cewa mutane biyu cikin uku a kasar ke fama da talauci na kin kari.

A wannan zaben akasarin 'yan takarar neman shugaban kasa sun ce zasu yi ruwa da tsaki wurin habaka tattalin arzikin kasar muddin suka samu nasara. Su ma 'yan kasan basu yi shiru ba. Suna shaidawa 'yan takarar batun habaka tattalin arzikin kasar.

Wasu na cewa duk da karfen uranium da man fetur da suke dashi amma suna cikin mummunar fatara da kuncin rayuwa. Basu da wutar lantarki alhali kuwa da uranium din kasar Faransa ke samarda wutar lantarki tana kuma sayarwa kasashen turai.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG