Biyo bayan sake bullar ci gaba da kai sabbin hare haren kunar bakin wake da ma kwantan bauna da ‘yan bindigar Boko Haram suka sake bullo da shi. Yan Najeriya sun fara tunananin irin nasarar da a baya ake ganin an cimma a yaki da ta’addanci.
Daraktan watsa labarai na hedikwatar sojojin Najeriya, Kanal Sani Usman Kuka Sheka, yace sanin kowa ne an sami nasara a yaki da ake da ta’addanci, inda aka shawo kan matsalar Boko Haram, samun wasu ‘dai ‘dai kun matsalolin tsaro ba yana nufin rashin samun nasara ba. sojoji da jami’an tsaro na yin bakin kokarinsu don tabbatar da ganin anyi maganin matsalolin.
A cewar tsohon gwamnan mulkin soja a jihohin Kano da Benue, Kanal Aminu Isa Kwantagora, idan ba kai ga lokacin da ‘yan ta’adda suka mika kansu domin a yi musu afuwa ba, tabbas za a rinka samun hare hare jifa jifa domin su nuna cewa sunanan.
Shi kuma Aliko El-Rashid Harun, na ganin a duk duniya babu inda za ayi amfani da karfin soja domin kawo karshen ‘yan ta’adda.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5