Na Ikra ya hadu da ‘Dan Iya, inda ‘Dan Iya yace ai tun da aka gama zabe nake ganin Kanawa sun riga sun darje, don kuwa naga sunyi sa’a gwamnan su shine Ganduje, kaga kuwa tunda da shi akayi gwamnatin Kwankwaso har zuwa lokacin da ta baje, shikenan zai ci gaba ne da duk aikin da aka fara a baya don goge dukkan ‘kauje.
Sai kawai na ji kwatsam ya bada Naira miliyan ‘dari da tamanin don kawai aje ofishin mataimakin sa a gurgurje, duk ko da yake ba’a dade da gina ginin a Naira miliyan ‘dari uku da ‘dan ‘doriya ba kuma a gurjuje, gashi ko bai ce komai ba lokacin da ake wancan gini duk ko da yake yana cikin gwamnatin ya saje shine nake ganin cikin wannan nadin kuwa babu lauje? Ace anyi gwamnati da kai a baya ace harma an baka mulkin ka gaje, amma kana neman barin mutanen da suka zabe ka da shan jaje?
Na Ikara yace, Eh ‘Dan Iya lalle nima naji labari, ance ma ya kori wasu ma’aikatan tsafta mata da samari, wanda yace musu aikin da suke wa gwamnati ya kamata su gane yanzu kan bata da marari, don haka yace su koma gida su ‘dau hakuri, shiyasa wasu ke ganin idan dai wannan shine canjin da aka zaba to akwai ha’dari, saboda ana kokarin maida mai Jaki ya koma kan kuturi, don haka ne ma nake ganin dole ne gwamnan ya sake nazari saboda wannan tsari yana da tsandauri, idan ko ba haka ba to ya tuna yana fa da sauran buri. Su kuwa Kanawa kowa yasan tarihin su kan siyasa tun tun da wuri.
‘Dan Iya yace, to yakamata duk wanda aka zaba a harkar siyasa ya sani idan kunne yaji to gangar jiki ta tsira, don ko siyasa ba ruwanta da wane yayi furfura, koko mutum yace ai babu komai Allah ya kaimu ranar zabe don na tara Naira, saboda masu zaben nan suna kallon kowa kuma suna zaune suna jira idan akaje filin zuba zabe fa sai sun ‘kyarkyra su gane waye na garin da zasu zaba kuma su waye zasu tura shara? Don da zarar sunga sun ci wuya gurin wanda suka zaba to zakaji suna ‘dan bakara’ su ma gwammace koda za’a ce sun tafka asara, gwamma su gwada wani idan sabon zabe yazo Allah barshi sayi sa’a ace gara-gara.
Saurari cikakkiyar hirar ‘Dan Iya da na Ikara.