Ibrahim Adamu wani matashi ne wanda yakasan ce, bai samu damar zuwa makarantar boko ba, a lokacin da yake karami. Domin kuwa yanzu shekarunsa sunja, yakai kimanin shekaru gomasha takwas, amma yanzu yake makarantar firamari.
Baya ga karatu yakan yi aikin wankin mota idan hakan ya samu, yana yin amfani da wanna kudi da yake samu wajen taimaka ma kansa, da abubuwan da zai bukata don zuwa makaranta. Kana kuma yakan aika ma iyayensa da wani abu a garinsu cikin jihar Jigawa, idan yasamu hali.
Ibrahim dai yana da burin yaga yasamu sana’a wacce zai dinga dogaro, da kanshi har ya taimaka ma sauran mabukata. Burin shi a rayuwa shine yaga ya kammala karatun sa, har ya shiga aikin soja, don yana sha’awar yayi aikin da zai taimakama kasar sa cikin gaskiya da amana.
Yana kuma fatar Allah yasa sauran matasa suyi amfani da damar da suka samu, don zuwa makaranta tunda kuriciyarsu batare da sun bari lokaci ya kure musu ba.