Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kunya ko Ilimi Kan Al-adar Diya Mace


Mata
Mata

Farkon fara ala’da ga mata, batu ne da ba kasafai aka cika yin magana akan sa ba musamman ma iyaye mata, bisa la’akkari da al’ada ta kunya da akan nuna a kasar Hausa.

Bayanai na nuni da cewa mafi aksarin ‘yan mata sukan fara al’adar ne ba tare da sun sami wani da zai yi musu bayanai na jagoranci ba yayin da wasu kadan kan samu irin wannan damar.

“Farko da yake kuruciya ne da na gani sai na rinka jin yaya ne, bana sha’awar abinci ga kasala.Da na fara gani, gaskiya ban gayawa mahaifiyata, saboda ina jin kunya.” In ji wata matashiya mai shekaru 22 da haihuwa.

A lokuta da dama kawaye na taka rawar gani wajen nunawa junansu yadda yanayin al’ada ta ke ta yadda idan ta same su ba za su dimauta ba.

“A wajen kawayena na koya, za a rinka yin hira a na cewa kaza da kaza, anan na koya, domin Mama na ba ta taba koya min ba, amma daga baya na gaya mata.” Matashiyar ta kara da cewa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG