Ra'ayin Bill Gate Ya Banbanta Da Sauran Kamfanonin Fasaha Kan Apple

Manyan kamfanonin fasaha sun fara tofa albarkacin bakinsu a takun sakar da ake yi tsakanin kamfanin Apple da gwamnatin Amurka, inda ra’ayin Bill Gates wanda ya kafa kamfanin Microsoft ya banbanta da na sauran.

Yayinda shugabannin kamfanonin fasaha da dama suka bayyana goyon bayan shugaban kamfanin Apple Tim Cook, Gates ya bayyana sabanin ra’ayi kan batun jiya Talata.

A wata hira da mujallar Financial Times tayi da shi, Gates ya ja a kan damuwar da Cook ya nuna cewa samar da wata manhajar da zata bude wayar daya daga cikin wadanda suka kai hari a San Bernardino, California a harin kan mai uwa da wabin da aka kai, zai zama hanyar bude wata waya samfarin iphone. Yace, ba cewa suka yi suna neman wani abu na gama gari ba, suna neman abinda ya shafi waya daya ne.

Bayaninsa ya sabawa na sauran manyan shugabannin kamfanonin fasaha a Silicon Valley da suka hada da na shugaban kamfanin Google Sundar Pichai da na Facebook Mark Zuckerberg, wadanda suka fito suna goyon bayan Apple.

Daga baya Gates ya shaidawa labaran Bloomberg cewa a karshe duka kotuna ne zasu yanke yanke hukunci kan batun.

A halin da ake ciki kuma, magoya bayan Apple suna shirin gudanar da zanga zanga a sama da birane 409. Wata kungiya dake hankoron kare yancin kafofin sadarwa da ake kira Fight for the Future, ta shirya gangamin a shagunan Apple dake birane da suka hada da New York da San Francisco da Minneapolis da Hong Kong da kuma London.

Hukumomi suna so kamfanin Apple ya taimaka masu su bude wayar da Syed Rizwan Farook ya yi amfani da ita, wanda shi da matarsa Tafsheen Malik suka kashe mutane 14 bara a San Bernardino, California.

Kamfanin Apple yaki, bisa hujjar cewa, neman bin bayan fage ne a matakan tsaron da kamfanin ya dauka, yace idan ya shiga hannun da bata gari nan gaba, zai iya zama da hadari ga masu amfani da wayoyin Apple.