Ra’ayoyin ‘Yan Ghana Mazauna Najeriya Kan Zaben Shugaban Kasa

  • Hasan Tambuwal

Zaben Ghana

A yayin da zaben shugaban kasar Ghana yake kusantowa Muryar Amurka ta tattauna da wasu ‘yan Ghana mazauna Najeriya don jin ra’ayoyinsu da fatan su a kan wannan zabe

Musa Kalamu sarkin ‘yan kasar Ghana mazauna Najeriya a garin Ibadan, jihar Oyo ya ce fatansu shi ne Allah ya sa a yi zaben lafiya a kuma kare shi lafiya.

Ya ce suna rokon Allah ya kawo zaman lafiya a Ghana. Allah ya kuma kare dukkan masifu ko ina a duniya.

Ya ce duk wanda ya samu nasara su na maraba da shi, inda ya kara da cewa babu bambancin Kirista da Musulmi yayin zaben.

Abdulwahab Alasan shima ya ce ya na fatan a yi zaben lafiya, babu tashin hankali inda ya yi wa duk wanda ya lashe zaben fatan alkhairi.

Ya kuma bayyana bukatarsa ga duk wanda ya lashe zaben yana mai cewa ana rikicin sarauta a yankin da ya fito a Ghana saboda haka yana son duk wanda ya lashe zaebn ya kawo karshen rikicin.

A nasa bangaren Amadu Isa ya yi addu'a Allah ya zabar musu shugaba da zai kawo musu ci gaba da kwanciyar hankali da arziki.

Ita kuwa Alhasan Nuriya ta ce fatanta a gyara musu gari a samawa mata aiki, yara su samu zuwa makaranta, kowa ya samu saukin rayuwa.

Sai Hajiya Ramatu Zakaria wadda ta ce fatanta alheri da zaman lafiya. Ta ce a rage kudin makaranta, a gyara hanyoyi, a kuma rage tsadar kayan amfanin yau da kullum.

Sauari cikakken rahot daga Hassan Tambuwal:

Your browser doesn’t support HTML5

Ra’ayoyin Wasu ‘Yan Ghana Mazauna Najeriya Akan Zaben Shugaban Kasarsu Da Ya Gabato.mp3