Matakin na ECOWAS ya zama abun nazari da tattaunawa ga masu sharhi inda wasu ke cewa kungiyar ta yi tsauri yayin da wasu ke cewa daidai ne.
Shugaban majalisar amintattu ta kungoyoyin arewa Nastura Ashir Sharif na cewa matakin zai takura rayuwar talakawa ne da yiwuwar fadawa irin yanayin fitinar kasar Sudan.
Nastura Sharif ya ba da shawarar kafa kwamitin dattawa na tsoffin shugabannin kasashen ECOWAS don su je Niamey su samar da maslaha.
Shi kuma Shu'aibu Gabchari wanda tsohon shugaban karamar hukumar Darazo ne a jihar Bauchi ya ce ya goyi bayan ECOWAS don ta hakan ne za'a sami sakamako a takadirin lokaci.
Gabchari ya bugi kirjin cewa duk jama'ar Afirka na marawa shugaba Bazoum baya.
A na sa sharhin dan jamhuriyar Nijar mazaunin Abuja Abubakar Khalidou ya ce Bazoum ya yi karambani a kalaman da ya furta na neman janyewa daga Faransa.
Khalidou ya ce bai yi mamakin abun da ya faru ba don Nijar mutum biyu ke mulki da babba da karami.
Hakanan Khalidou ya bukaci a bar sojojin su shekara biyu kan karagar mulki kafin sanin mataki na gaba.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5