R. Kelly Zai Koma Kotu Kan Zarginsa Da Yin Coge A Shari’arsa Ta 2008

R. Kelly Zai Koma Kotun Don Zarginsa Da Yin Magudi A Shari’arsa Ta 2008

An fara zaben masu taya alkali ne yau litinin a shari'ar da gwamnatin tarayya ke wa R. Kelly a garinsa na Chicago, inda shahararran mawakin na R&B ke fuskantar tuhuma kan zarginsa da yin danne gaskiya a shari'ar da aka masa kan aikata lalata a jihar a shekara ta 2008.

WASHINGTON, D.C. - Kelly ya na fuskantar tuhuma kan zarginsa da hana gaskiya aikinta ta hanyar yin barazana da kuma biyan wata yarinya da ya dauki bidiyon yadda ya yi lalata da ita lokacin da yake wajen shekara 30, kuma ita ba ta wuce 14 ba.

Alkalan kotun sun wanke Kelly kan duk wasu tuhume-tuhume da ake yi masa a waccan shari’a ta 2008, wasu kuma daga baya sun bayyana cewa ba su da wani zabi domin yarinyar ba ta bayar da shaida ba. Matar, yanzu ta cika shekara 30, za ta zama uwar bada shaida ta gwamnati a shari'ar tarayya mai zuwa.

R. Kelly Zai Koma Kotun Don Zarginsa Da Yin Magudi A Shari’arsa Ta 2008

Kelly, mai shekaru 55, ya shiga kotun tarayya a birnin Chicago a yau Litinin inda da wani alkali na birnin New York ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari saboda samunsa da laifin yin amfani da mukaminsa wajen lalata da wasu matasa magoya bayansa.

Kelly, wanda ya fito daga cikin talauci a Kudancin Chicago, ya zama mawaƙi, babban tauraro, marubuci kuma mai shiryawa, yana fuskantar tuhume-tuhume da yawa a shari'ar tarayya. Sun hada da tuhume-tuhume hudu na yaudarar yara kanana don yin lalata da su.

-AP