Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Sakkwato ta kara neman shigowar kasar Qatar, domin taimaka wa talaka a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya a fannin kawar da fatara, inganta ilimi da dai sauransu.
Halin matsi da ‘yan Najeriya suka samu kansu ciki ya jima yana ci musu tuwo a kwarya duk da cewa gwamnatocin da suka gabata sun ce suna kokarin kyautata rayukan jama'a. Sai dai kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu.
Wannan yanayi hadi da wasu matsaloli kamar rashin tsaro, cire tallafin man fetur da makamantansu ba su rasa nasaba da yadda jama'a ke ta wahala wajen neman saukin rayuwa
Sababbin gwamnatoci da suka kama aiki a jihohin kasar suma sun dukufa wajen kyautata rayukan jama'a da abinda suke samu, sai dai kuma wasu na neman shigowar wasu kasashe domin samun biyan bukata.
Gwamnan jihar Sakkwato Ahmad Aliyu Sokoto wanda ya fitar da ajandodi tara da zai yi aiki da su, ya nemi kara shigowar gwamnatin kasar Qatar ta hannun jakadanta a Najeriya, Dokta Ali Bin Ghanem Al-Hijri, domin saukaka halin da jama'a suke ciki ko ba komai hukumar kididdiga ta Najeriya ta sha ayyana jihar a zaman mafi talauci.
Jakadan Qatar a Najeriya Dokta Ali bin Ghanem Al-Hijri ya ce kasarsa za ta ci gaba da kyakkyawar hulda da Najeriya domin taimaka wa marasa karfi.
Ya ce da yake akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Qatar da Sakkwato inda ake aiwatar da ayukka da dama, a wannan shekara da na shekara mai zuwa zamu kara dinke zumunci dake tsakaninmu, mun zu da hannu a bude domin kara taimaka wa talaka.
Da ma kasar Qatar ta jima tana taimaka wa kasashen duniya inda jihar Sakkwato ta yi ta samun taimakonta a fannin Ilimi, kawar da fatara , kula da kiwon lafiya, bunkasa ilimi da makamantansu, akan haka ne masu lura da lamurran yau da kullum ke ganin akwai bukatar yin cikakken amfani da tallafin da kasar ke bayarwa domin a samu biyan bukatun bayar da tallafin.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5