Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Kokarin Bunkasa Al’adunta A Qatar

Jakadan Najeriya a Qatar, Ambasada Yakubu Abdullahi Ahmed, hagu, da Shugaban kwamitin al’adu na Katara, Farfesa Khalid Ibrahim Al Sulaiti, dama.

Kauyen al’adu na Katara na da wuraren nuna al’adu na kasashe daban-daban  na duniya, inda yake dauke da gine-gine da suka hada da; wurin kallo, otel-otel, masallatai da sauransu.

Najeriya ta bukaci aiki tare da hukumar al’adu ta kasar Qatar mai suna Karata wajen bunkasa al’adun Najeriya a kasar ta Qatar.

Jakadan Najeriya a Qatar, Ambasada Yakubu Abdullahi Ahmed, ya nemi wannan bukata yayin da ya kai ziyara ofishin shugaban kwamitin al’adu na Katara, Farfesa Khalid Ibrahim Al Sulaiti a Doha, babban birnin kasar.

Kauyen al’adu na Katara na da wuraren nuna al’adu na kasashe daban-daban na duniya, inda yake dauke da gine-gine da suka hada da; wurin kallo, otel-otel, masallatai da sauransu.

Jakadan Najeriya a Qatar, Ambasada Yakubu Abdullahi Ahmed, hagu, da Shugaban kwamitin al’adu na Katara, Farfesa Khalid Ibrahim Al Sulaiti, dama.
Jakadan Najeriya a Qatar, Ambasada Yakubu Abdullahi Ahmed, hagu, da Shugaban kwamitin al’adu na Katara, Farfesa Khalid Ibrahim Al Sulaiti, dama.

Ambasada Ahmed ya bayyana yadda Najeriya ke da al’adu masu dumbin yawa, wadanda idan ofishin jakadancin ya hada kai da hukumar al’adu ta kasar ta Qatar za su taimaka wajen kara dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaban hukumar al'adun na Qatar dai ya ce Ofishin Jakadancin na iya amfani da kauyen al’audun wajen nunawa duniya al'adun kasar, musamman bayan an kammala gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.

A ranar 21 ga watan watan Nuwambar bana za a fara karawa a gasar ta cin kofin duniya, ko da yake, Najeriya ba ta samu gurbin shiga gasar ba.

XS
SM
MD
LG