QATAR 2022: Siyasa Ba Za Ta Shiga Karawarmu da Iran Ba – Kocin Amurka

Kocin Amurka Gregg Berhalter

Kocin Amurka, Gregg Berhalter, ya ce harkar siyasa ba za ta shiga karawar Cin Kofin Duniya da tawagarsa za ta yi da Iran ba, biyo bayan cancaras da aka yi tsakanin Amurka da Ingila ranar Jumma’a.

Berhalta ya gamsu, bayan da ya ga yadda matasan ‘yan wasan Amurka, su ka jure fafatawa da shahararrun ‘yan wasan Ingila, har aka tashi ba ci, a filin Wasa na Al Bayt a rukuni na B.

Wannan sakamakon ya haifar da karawa, wadda ake dokin gani, tsakanin Amurka da Iran, ranar Talata mai zuwa, lokacin da duk wadda ta yi nasara tsakaninsu, za ta samu shiga zagayen na biyu.

Wannan fafatawar da ake begen gani, ta maimaita kanta ne kamar yadda ta kasasnce a Gasar Cin Kofin Duniya ta 1998, inda kasashen biyu masu adawar siyasa suka kara kana Iran ta yi nasara da ci da 2-1, fafatawar da aka kira da “Uwa ga duk wasannin Kwallon Kafa.”

Sai dai Berhalter ya dage cewa yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin gwamnatocin Amurka da Iran, siyasa ba za ta yi tsairi a karawarsu ta ranar Talata mai zuwa ba.

Berhlter ya ce “Na yi wasa a kasashen uku, kana na yi aikin horarwa a Sweden, kuma abin da ke faruwa a kwallon kafa shi ne zaka hadu da mutane daban daban daga ko’ina cikin duniya, amma kuma soyayyar wasa ta hada ku wuri daya."