Qatar 2022: Karawar Kamaru Da Switzerland

'Yan wasan Kamaru lokacin da suke atisye a Qatar 2022 (Hoto: Cameroon FA)

Rukunin na G a gasar cin kofin duniya ta Qatar, ya kunshi Brazil, Serbia, Kamaru da kuma Switzerland, saboda haka samun makin uku na farko na da matukar muhimmanci a wannan wasa na ranar Alhamis.

Karawa tsakanin Switzerland da Kamaru, wasa ne da zai zamanto dole kowacce kasa ta nemi nasara, duba da irin zakakuran tima-timan da ke rukunin.

Rukunin na G a gasar cin kofin duniya ta Qatar, ya kunshi Brazil, Serbia, Kamaru da kuma Switzerland, saboda haka samun makin uku na farko na da matukar muhimmanci a wannan wasa na ranar Alhamis.

'Yan wasan Switzerland a gasar nahiyar turai a 2020

Kamaru ta sha kaye sau uku a jere a wasannin da ta buga a gasar cin kofin duniya da aka yi a 2014 da 2010.

Switzerland kuwa, tana tunkaho da jarumatar da ta nuna a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, inda ta kai matakin quarter final a bara, sannan ta lashe wasanin shiga gasar, inda ta tserewa Italiya.