Hakan ya nuna alamar dorewar kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu duk da rashin tabbas din da ake dashi akan mamayar da rashan ta yiwa Ukraine tsawon fiye da shekaru 2 da rabi.
Sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon fadar kremlin dake ruwaito wayar tarho din da Putin ya bugawa Ramaphosa na cewar, "An bayyana fatan ci gaba da gudanar da ayyukan hadin gwiwa kan kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Rasha da Afirka ta Kudu a dukkan fannoni,"
Majalisar Dokokin kasar ce ta sake zaben Ramaphosa a Juma'ar data gabata. Saidai gazawar jam'iyyarsa ta African National Congress ta samu rinjaye a zaben watan daya gabata, karon farko cikin shekaru 30, ya sabbaba kafa gwamnatin gamin gambizar jam'iyyu biyar.
Kasashen Rasha da Ukraine sun yi ta sintirin neman samun goyon bayan kasashen Afrika tun bayan mamayar 2022, inda ministocin kasashen wajensu ke rangadi zuwa kasashen nahiyar.
-Reuters