PSG Na Jagorantar Teburin Gasar Faransa

Neymar

Dan wasan na Brazil ya yi amfani da dabarar nan tasa inda ya kidima mai tsaron ragar Monaco, Alexander Nuebel kafin ya buga kwallon ta barin hagu

Dan wasan Paris Saint Germain, Neymar ya zura kwallo daya ga kungiyarsa ta hanyar bugun fenariti inda suka tashi da ci 1-1 da Monaco a gasar Faransa ta Ligue 1.

Neymar ya yi amfani da kwallon da Messi ya doko masa ne daga barin hagun filin wasan, wacce ta ratsa ta tsakiyar mai tsaron bayan Monaco Guillermo Maripan wanda ya kwade shi daga baya.

Da farko alkalin wasan ya yi biris da abin da aka ma Neymar, amma bayan da aka kalli bitar kwallon a bidiyo sai ya amince da bugun fenariti.

Dan wasan na Brazil ya yi amfani da dabararsan nan inda ya kidima mai tsaron ragar Monaco, Alexander Nuebel kafin ya buga kwallon ta barin hagu.

Wannan ce kwallo ta shida da Neymar ya ci a gasar cikin wasannin biyar da suka buga

Yanzu PSG na da maki 10 kuma ita take jagorantar teburin gasar inda ta dara abokiyar hamayyarta Marseille da yawan kwallaye da kuma kungiyar Lens.