Prime Ministan kasar Italiya, Silvio Berlusconi ya baiyana tababa sosai gameda tsoma bakin da kungiyar kawancen tsaro ta NATO tayi a rikicin Libya. Prime Ministan yayi wannan furucin ne a yayinda gwamnatinsa ta masu ra'ayin rikau ta bada sanarwar shirye shiryenta na rage gudumawar da take bayarwa a yakin da ake gwabzawa a Libya.
Alhamis din nan Mr. Berlusconi, yace shi dama baya goyon bayan wannan yaki, to amma babu abnda zai iya yi, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta bada umarnin haramta zirga zirgan jiragen sama a sararin samaniyar Libya, domin kare farar hula a kasar. Prime Ministan na Italiya, wanda shine shugaban wata kasar turai, na farko daya fito filli ya baiyana tababa gameda samun nasarar wannan yaki, yana fuskantar matsin lambar janye sojojin kasar daga babar kawarsa Northern League..
A halin da ake ciki kuma, anan birnin Washington DC, da kyar Majalisar wakilai ta samu nasara akan matakin, wanda in da ace an zartar, to daya rage kudin da Amirka take kashewa akan hidimomin soja a Libya daga daya ga watan oktoba idan Allah ya kaimu.
To amma Majalisar ta jefa kuri'ar hana amfani da kudaden Amirka wajen horas da, ko kuma sayawa yan tawayen Libya makamai. Wannan doka, ta kuma tanadi samun amincewar Majalisar dattijai da sanyan hannun shugaba Barack Obama kafin ta zama doka.