Ficerwa da kasar Philippines ta yi daga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ya janyo zargi daga masu lura da al'amura, wadanda suke ganin matakin na da nasaba da kokarin kaucewa dokar da za ta hana shirinsa na yaki da masu mu'amulla da muggan kwayoyi.
WASHINGTON D.C. —
Wani mataki da kasar Philippines ta dauka wannan watan na janyewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ya janyo zargin cewa kusoshin gwamnatin kasar na kokarin jaddada matakin yaki da masu safarar kwayoyi a kasar.
A makon da ya gabata ne Shugaban kasar Philippine Rodrigo Duterte ya janye dokar da ta ba da damar kafa kotun amman ofishin sa da kotu sun ba da bayanai daban daban.
Ita dai wannan Kotun da aka kafa a shekarar 2002, tana hukunta laifuka kamar kisan kiyashi da kuma laifukkan yake-yake.
Masu kare hakkin dan adam sun yi zargin cewa yaki da masu harkar muggan kwayoyin da shugaba Duterte yake wanda ya kai tsawon shekaru biyu ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a hannun ‘yan sanda.