Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban 'Yan Siriya Na Barin Ghouta


'Yan gudun hijirar Siriya da ke barin Ghouta
'Yan gudun hijirar Siriya da ke barin Ghouta

A wani al'amari mai ban jimami, dubban farar hula na gudu su na barin yankin Ghouta duk kuwa da yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka ce an cimma kwanaki.

Dubban mutane, da su ka hada da maza da mata da yara, sun gudu daga yankin Ghouta na gabashin Siriya jiya Alhamis.

Ganin yadda yaki ke ta tayar masu da hankali, mutanen sun goya kayakinsu a baya, wasu rike a hannuwa, wasu kuma jibge kan kekuna ko kuma motocin daukar kaya, ana ta neman mafaka.

‘Yan tawaye sun rike gabashin Ghouta tun daga shekarar 2012, to amma yanzu sojojin Siriye ne ke rike da akasarin yankin bayan da su ka yi ta ruwan wuta da kuma hare-haren jiragen sama a hanyin.

Peter Maurer, Shugaban kungiyar agaji ta Red Cross, ya fadi a wani bayani cewa ziyarar da ya kai Siriya kwanan nan ta yi, abin da ya kira, “kara jaddada fargabarsa cewa yakin da ake yi a yankin ya kai wani mataki mai ban tsaro.” Ya kara da cewa, “Yawancin lokaci burin shi ne a lalata abubuwa ta yadda ba a ma damuwa da halin da dan adam ke ciki.”

Shugaban kungiyar rajin kare hakkin dan adam a Siriya mai hedikwata a Burtaniya, ya fadi jiya Alhamis cewa kaurar da mutane ke yi yanzu daga wannan yankin da aka yi wa kawanya, wanda kuma ke kusa da birnin Dimashku, ta wuce wadda aka taba gani tun bayan da gwamnati ta kaddamar yakin sake kwato yankin a watan jiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG