Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa , dan takararar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Labour Party a Najeriya, Peter Obi, ya bayyana sunan wanda zai masa takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.
Obi ya bayyana Datti Baba-Ahmed a matsayin abokin takararsa a ranar Juma’a a Abuja, babban birnin Najeriya.
Yayin sanar da sunan Baba-Ahmed, Obi ya ce, lokaci ya yi da za a kubutar da Najeriya don ta zama kasa abin koyi.
“An sha yi a kasashe masu tasowa da dama, ba wani abu ba ne mai sarkakiya.
“Mu matasa ne, masu jini a jika, za kuma mu dukufa wajen ganin mun mayar da makeken yankin arewa tushen hanyar samun man fetur a nan gaba. In ji Obi.
Ya kara da cewa, jihar Kano da Kaduna, za su zama cibiyoyin sarrafa kayayyaki a Najeriya.
Obi ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa Baba-Ahmed zai yi amfani da dumbin iliminsa wajen ganin an cin ma burin da suka sa a gaba na ‘Rescue Nigeria Project’ – wato shirin kubutar da Najeriya don a kyautata makomarta.
Baba-Ahmed, wanda shekarunsa ba su kai hamsin ba, shi ne mamallakin jami’ar Baze University da ke Abuja da kuma jami’ar Baba-Ahmed da ke Kano.