Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence, ya yi kakkausar suka ga kasashen Turai kawayen Amurka, kan matsayinsu game da Iran da Venezuela, a wani jawabin da ya yi a wani babban taron da aka yi a Munich, kasar Jamus game da batutuwan tsaro.
“Lokaci ya yi da ya kamata kawayen Amurka na Turai su daina yin zagon kasa ma takunkumin da Amurka ta kakaba ma wannan gwamnati mai yawan kisa da kuma jirkita tsari. Lokaci ya yi da ya kamata kawayenmu na Turai su janye daga yarjajeniyar nukiliyar Iran” Inji Pence.
Ya kuma yi kira ga kawayen Amurka da su amince da madugun ‘yan adawa Juan Guaido a matsayin Shugaban Venezuela na halas.
Tuni kasashen Turai sama da 20 su ka yi hakan, to amma kungiyar Tarayyar Turai ba ta ida amincewa da Guaido a matsayin Shugaba.
Da dama na ganin Nicholas Maduro, wanda ake takaddama kan halarcin Shugabancinsa, da magudi ya ci zaben bara, a yayin da kasar ke fama da fatara da tsadar kaya.