Pelosi Na Shirin Mika Batun Tsige Trump Ga Majalisar Dattawa

A yau Laraba ake sa ran Majalisar wakilan Amurka za ta kada kuri'a kan batun tura takardun hujjojin tsige shugaban Amurka Donald Trump, zuwa ga majalisar dattawan kasar, don fara zaman shari’ar da ake sa ran farawa a makon gobe.

Shugaban Kasar Aurka Donald Trump

Majalisar ta amince da takardun hujjojin ne a watan da ya gabata, amma kakakin majalisar Nancy Pelosi, ta jinkirta tura takardun yayin da 'yan Demokrat a majalisar wakilai, suka yi kokarin ganin shugabannin majalisar dattawa sun yarda a saurari bahasi daga wasu sabbin shaidu a lokacin zaman shari’ar.

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa Mitch McConnell

Har yanzu dai ba a warware batun ba. Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa Mitch McConnell, ya ki yarda da matakin kiran shaidun, kuma ya ce za a yanke wannan shawarar daga baya a yayin da ake shari’ar.