Diego Maradona ya sake yin kaca-kaca da gwarzon kafar Brazil Pele, yana mai cewa watakila dai Pele "bai sha maganin da likita ya ba shi" ba ne shi ya sa yake fadin cewa Neymar ya fi Lionel Messi iya buga kwallo.
Da yake magana ranar alhamis a Dubai, Maradona yace lallai da gaske Neymar dan kasar Brazil ya iya kwallo, amma kuma ai ko da wasa ba zai iya kamo kafar Lionel Messi ba, dan kasar Argentina da ake jin cewa a bana ma shi zai zamo zakaran kwallon kafa na duniya a shekara ta uku a jere.
Da ma dai Maradona da Pele sun saba kai ruwa rana da junansu. A bara ma, mutanen biyu sun yi zage-zage a lokacin da Pele yace Maradona bai iya koyar da wasa ba saboda yadda ya tafiyar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina a gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta 2010.
A wannan karon, Pele yace Neymar ya fi Messi basirar kwallon kafa, amma yace dole ne matashin dan Brazil ya zage ya nunawa duniya basirarsa idan yana son ya zamo zakaran kwallon kafar duniya nan gaba. Wannan kalamin bai yi dadi a kunnen Diego Maradona ba, wanda a yanzu shi ne mai koyar da wasa na kungiyar kwallon kafa ta Al Wasl ta Hadaddiyar Daular Larabawa.
A cewar Maradona, "da alamun Pele bai sha maganin da ya dace ya sha ba, maimakon ya sha maganin barcin da aka ba shi da tsakar dare sai ya sha wanda ake ba mutum idan ya tashi daga barci. Wannan shi ya sa ya rude, ya kasa sanin abinda ya fada."
Maradona ya ba Pele shawarar da ya, "rika shan maganin da likita ya ce masa, kuma ya sauya likitansa, kafin yayi magana irin wannan."
Har yanzu dai ba a ji amsar da Pele zai mayar game da wannan kalami na baya-bayan nan daga bakin Maradona ba.