Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaya Toure Shi Ne Gwanin Gwanayen Kwallon Kafa Na Afirka


Yaya Toure na Manchester City a lokacin wasansu na Premier League na Ingila da Liverpool a filin wasa na Anfield Stadium a ranar 27 Nuwamba, 2011.
Yaya Toure na Manchester City a lokacin wasansu na Premier League na Ingila da Liverpool a filin wasa na Anfield Stadium a ranar 27 Nuwamba, 2011.

Dan wasan tamaular na kungiyar Manchester City da kuma kasar Ivory Coast ya doke Seydou Keita na Mali da Andre Ayew na Ghana

Dan wasan kwallon kafar kasar Ivory Coast ko Cote D'Ivoire, Yaya Toure, shi ne gwanin gwanayen kwallon kafa na nahiyar Afirka a wannan shekara.

JIya alhamis aka nada masa wannan sarauta a wani bukin da aka yi a birnin Accra a kasar Ghana.

Gwanin tamaular na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a kasar Ingila, wanda a bana yake tayar da kura hagu da dama, ya doke Seydou Keita na kasar Mali da Andre Ayew na kasar Ghana wajen zamowa gwanin gwanayen kwallon kafa na nahiyar Afirka.

Keita, wanda yake taka kwallo ma kungiyar FC Barcelona ta kasar Spain, shi ya zo na biyu, yayin da kaninsu Ayew dake buga kwallo a kungiyar Olympique Marseille ya zo na uku.

A cikin wannan shekara, Toure ya taimaka ma kungiyarsa wajen lashe kofin kalubalenka ta kasar Ingila, watau FA Cup, ta hanyar jefa kwallo na karshe a ragar kungiyar SToke City.

A bayan da ya bar kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona, Toure ya zamo daya daga cikin 'yan wasan da kungiyar Manchester City take tinkaho da su a saboda yadda masana suka ce ya iya taka kwallo da rike ta, da kuma basirarsa mai kaifi wajen iya karanta yadda wasa ke tafiya.

Haka kuma, Yaya Toure, yana daya daga cikin 'yan wasan da suka taimaka ma kasar Ivory Coast har ta samu nasara a wasannin share fagen Gasar Cin Kofin kasashen Afirka ta 2012.

XS
SM
MD
LG