Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Didier Drogba Zai Komo Amurka?


Didier Drogba na kungiyar Chelsea a lokacin da ya jefa kwallon farko cikin ragar Leverkusen ta Jamus a wasan Champions League na rukunin E da aka yi ranar laraba 23 Nuwamba, 2011 a tsakanin Bayer Leverkusen da Chelsea FC a kasar Jamus.
Didier Drogba na kungiyar Chelsea a lokacin da ya jefa kwallon farko cikin ragar Leverkusen ta Jamus a wasan Champions League na rukunin E da aka yi ranar laraba 23 Nuwamba, 2011 a tsakanin Bayer Leverkusen da Chelsea FC a kasar Jamus.

Wakilin dan tamaular yace Chelsea ta yi musu tayin kwantarakin karin shekara daya, amma sun ce a kai kasuwa

Wakilin shahararren dan tamaula Didier Drogba, yace maigidan nasa yana shirin jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda idan kwantarakinsa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ya kare a karshen wannan kakar kwallon kafa ta Premier League.

Thierno Seydi, wakilin Drogba, yace Chelsea ta yi musu tayin karin shekara guda, amma ba su gamsu da hakan ba, har ma ya fadawa 'yan jarida cewa, "mun san abinda muke so, mun san inda muke son zuwa, mun kuma san irin tayin da aka yi mana."

Wakilin na Didier Drogba yace zasu ci gaba da neman wata kulob din da zata ba su kudi fiye da wanda Chelsea ta yi musu tayi.

Seydi yace watakila Didier Drogba zai waiwayi Amurka domin buga tamaula a wasannin Major League Soccer domin kungiyar kwallon kafa ta L.A. Galaxy ta nuna sha'awar daukarsa. Idan ba a mance ba, David Beckham ma yana buga ma kungiyar ta Galaxy dake birnin Los Angeles a Jihar California, wadda ta zamo zakarar MLS a 2011.

Wakilin na Drogba, Seydi ya ce, "LA Galaxy na daya daga cikin wuraren da (Drogba) ke son komawa. An yi maganar kungiyar Anzhi Makhachkala ta kasar Rasha ma domin tana biyan albashi mai tsoka, amma dai kungiyar ba ta tuntube ni ko kuma Didier da wani tayi ba."

Kungiyar AC Milan ma ta nuna sha'awar daukar dan wasan na kasar Ivory Coast mai shekaru 33 da haihuwa, amma kuma wakilinsa yace a wannan lokaci, babu wani abinda Drogba zai yi kokarin nunawa duniya a fagen tamaula, zai nemi kulob ce wadda za ta ba shi kwantaraki mafi tsoka.

Wakilin yace tun farko AC Milan ta nemi da a ba ta aron Drogba ne, amma kuma bisa sharadin cewa idan ta ga ya dace tana iya sayensa, amma sai suka ki yarda da hakan.

Masu sha'awar kwallon kafa dai sun zuba ido su ji, su kuma ga inda Drogba zai dosa. Shin da sauran wasa a jikinsa?

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG