Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Yobe tace zata kauracewa zaben kananan hukumomin da jam'iyyar APC mai mulkin jihar zata kaddamar a karshen makon nan.
WASHINGTON, DC —
Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Yobe tace zata kauracewa zaben kananan hukumomin da jam'iyyar APC mai mulkin jihar zata kaddamar Asabar din nan.
Shugaban matasa na jam'iyyar PDP wanda dan asalin jihar ta Yobe ne Ado Adamu Bunu-Yadi, yace idan za'a kafa gwamnati a zauna lafiya shi suke so. Yaci gaba da cewa a Yobe da makaho da mai ido da babba da yaro, kowa yasan jihar bata da cikakken zaman lafiya da zai sa ta shiga gudanar da zabe ba.
Shugaban matasan yace kamar shi daga yankin Gujba, ba da jumawan nan bane aka kashe dalibai kusan 80 a wani koleji dake yankin, wata biyu kacal bayan haka ace za'a gudanar da zabe, ya nuna cewa gwamnatin jihar bata mutunta rayukan jama'a.
Maimakon kaddamar da zabe, yace jam'iyyar zata yi amfani da wadannan kudade wajen kafa masana'antu da zasu samarda ayyukan yi ga dubban matasa, wadanda yace a ganinsa rashin aikin yi yasa da dama daga cikinsu suke daukan makamai.
Ga karin bayani da ya yiwa wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5