Jihar Yobe tace ta shiryawa zaben yankunan kananan hukumomin ranar Assabar din nan
WASHINGTON, DC —
Duk da halin rashin kwanciyar hankalin da ake fuskanta da kuma zamanta daya daga cikin jihohin Nigeria ukku dake karkashin “Dokar Ta Baci”, jihar Yobe dake Arewa-maso-gabashin Nigeria tace ta shirya tsaf don gudanarda zaben yankunan kananan hukumomi a wannan Assabar. A can da, an so a sami rudami lokacinda shugaban Hukumar zabe ta Kasa (INEC), Prof. Attahiru Jega yace ba za’a iya gudanarda zabukka a jihohin dake karkashin dokar ta-baci ba, amma daga baya ya fayyace cewa wannan maganar tashi bata shafi zaben yankunan kananan hukumomi ba, wanda hakkin hukumomin zaben jihohi ne, ba na Hukumar zaben tarayya ba. Wakilin Muryar Amurka, VOA, Haruna Dauda Yaroh ya zanta da shugaban Hukumar zabe ta jihar Yobe, Mohammed Jauro, kan shirn zaben: