Nasarawa: PDP Za Ta Garzaya Kotu Kan Zaben Gwamna

Farfesa Mshmoud Yakubu Shugaban hukumar zaben Najeriya

Jami’iyyar PDP a jahar Nasarawa ta ce za ta je kotu saboda rashin gaskiya da ta ce anyi mata a zaben gwamna da aka gudanar makon jiya.

Shugaban jami’iyyar PDP a jihar Nasarawa, Francis Orogu ya ce jami’iyyar APC ta hada kai da hukumar zabe da jami’an tsaro wajen yi mata magudi a zaben.

Da yake mayar da martini, Sakataren jami’iyyar APC a jihar ta Nasarawa, Alhaji Aliyu Bello ya ce suna shirye don haduwa da jami’iyyar ta PDP a kotu.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Nasarawa, inda wakilyar sashen Hausa ta kira lambar kakakin hukumar amma bai dauki wayar ta ba.

A bangaren jami’an tsaro kuwa, kwamandan rundunar tsaron al’umma ta Civil Defence a jihar, Muhammad Gidado Fari ya ce basu hada kai da kowa ba, sun dai bada tsaro ne don gudanar da zabe mai tsabta a jihar.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Nasarawa: PDP Za Ta Garzaya Kotu Kan Zaben Gwamna - 2'34"