Sanata Mas'ud El-Jibrin Doguwa da Alhaji Rabiu Dan Sharu suka fafata akan neman kujerar shugaban jam'iyyar na jihar Kano har sai da aka jefa kuri'a.
Dr Sam Egwu shi ne wanda hedkwatar PDP ta turo domin gudanar da zaben. Bayan zaben ya bayyana sunan Alhaji Rabiu Dan Sharu a matsayin wanda yayi nasara da kuri'u fiye da dubu daya.
Sabon shugaban ya yiwa 'yan PDP albishir. Ya tabbatar wa 'yan jam'iyyar cewa zasu tabbatar da yin adalci tare da taimakon Allah a bisa duk matakai. Wanda suka yi takara tare da ya kira yayansu ya sa an yi masa aduu'a.
A sakonsa ga 'yan PDP jihar Kano da suke neman madafin iko a zaben shekara mai zuwa, ya kira su sa Allah gaba su tabbatar da cewa hikima da dabara ba zasu basu matsayin da suke nema ba idan Allah bai rubuta zasu samu ba.
Magoya bayan Sanata Doguwa sun ce an yi zabe lafiya kuma an gama lafiya amma iyayensu basu duba cancantar wanda ya cancanta ba. A bar 'yan jam'iyya. Kada ace wani zabi wani. A bar 'yan jam'iyya su zabi abun da suke so da Sanata Masa'udu yaci zaben.
To saidai shi Sanata Masa'udu yace babu wani abun da ya ji a cikinsa. Yace yayi takara kuma ba an yi kokari ne a dorawa mutane abun da basa so ba. Mutane ne suka yi zabe, suka nuna Rabiu Dan Sharu suke so a daidai wannan lokacin. Sabili da haka menene kuma zai kaishi ya tsaya yana wata magana. Yace shi ya amince da abun da aka yi kuma yana yi masa fatan alheri.
Sanata Masa'udu yace shi dan jam'iyya ne. Zasu yi aiki tare su tabbatar sun kawar da gwamnatin APC daga mulkin Kano a zaben 2015. Ashirye yake ya hada hannu da shugaban da aka zaba domin jam'iyyar taci gaba.
Sanata Muhammed Mana shi ne ya rike mukamin shugaban jam'iyyar na wucin gadi har aka yi zabe. Yace tun da 'yan takaran basu shirya ba yace a yi zabe. Dimokradiya ta gaji a yi zabe kuma an yi lami lafiya ba tashin hankali. An tara mutane fiye da dubu biyu amma komi ya tafi lafiya.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5