PDP Tayi Barazanar Ladaftar da 'Ya'yanta

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Taraba Mr. Victor Kona ya kaddamar da kwamitin neman zabe na jam'iyyar a jihar.

A cikin jawabin da yayi shugaban jam'iyyar yayi barazanar cewa zasu ladaftar da duk wadanda su ke nunawa suna tare dasu amma suna yi masu zagon kasa.

Barazanar tashi na zuwa ne yayin da tsohon mukaddashin jihar Alhaji Garba Umar UTC ya ajiye kujerar takarar sanata a karkashin jam'iyyar ta PDP wadda shugabannin jam'iyyar suka yi masa tayi a Abuja. Lamarin ya jawo cecekuce. Amma tuni jam'iyyar ta mika kujerar takarar ga mukaddashin gwamnan jihar na yanzu Alhaji Sani Abubakar Danladi.

Kodayake mutane na ganin abun da ya faru tamkar baraka ce a jam'iyyar, amma shugabanta na jihar yace babu wata baraka a jam'iyyarsu. Yace an yi zaben fidda gwani kuma ba kwace kujerar aka yi daga Alhaji Umaru Garba UTC ba.

Kamar jam'iyyar PDP din ita ma APC tana da nata matsalar a jihar. Tana fama da rikicin cikin gida inda wasu kusoshinta musamman bangaren Buhari suke zargin cewa shugabansu na jihar da 'yar takararsu ta kujerar gwamnan suna yiwa jam'iyyar zagon kasa. Daya daga cikin 'yan Buhariya Alhaji Sani Tullu yana cewa babu shakka ana yi masu barazana domin su mutanen Buhari ne. Yace suna kokarin su hanasu janye mutane da masu yi masu barazana suke son yin anfani dasu ta hanyar kudi domin su bi hanyar da bata gaskiya ba ce.

Alhaji Tullu yace akwai masu yiwa PDP aiki a jam'iyyarsu. Ko shugabansu PDP yake yiwa aiki. Ita ma 'yar takarar tasu PDP ta keyi wa aiki.

A martanin da ya maida shugaban APC na jihar Taraba Alhaji Hassan Nikardo yace daya bangaren ne yake yiwa jam'yyarsu zagon kasa. Yace an san cewa Alhaji Sani Tullu yana yiwa jam'iyyar zagon kasa kuma za'a dauki mataki daga inda ya fito. Munafincinsa ya sa yana kawow ajam'iyyar fitintinu. Ya kira duk wani munafiki yayi hattara. Yace sun wuce lokacin da zasu lallaba mutane.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Tayi Barazanar Ladaftar da 'Ya'yanta - 3' 21"