PDP Na Zargin APC Zata Murde Zaben Bayelsa da Taimakon INEC

PDP

PDP ta fara zargin APC da shirin yin magudi a zaben Bayelsa da taimakon INEC wai kamar yadda tayi a jihar Kogi.

PDP tace yanzu ya rage ga hukumar zabe wato INEC ta fuskanci duk wata fitina da ta taso a zaben jihar Bayelsa domin ita ta jawo inji mai magana da yawun jam'iyyar.

Yace suna da labarin gwamnatin APC ta umurci hukumar zaben ta murde sakamakon zaben jihar Bayelsa kamar yadda ta yi a jihar Kogi.

Kakakin PDP Oliseh Metuh ya kara da cewa kama shugaban gidan telebijan na AIT wata hanya ce ta rufe bakin 'yan adawa. Yace suna da hujjar cewa gwamnati ta hannun sakataren gwamnatin tarayya ta ba hukumar zabe umurnin murde zaben.

Yace haka ma hukumar EFCC ta zama kotu ta zama alkali domin ta je ta damke Mr. Dokpesi kan zargin da ba'a tabbatar ba. Yace sun san akwai wasu 'yan PDP da ake shirin kamasu da sunan sun wawure kudin al'umma.

Akan ko yana ganin an kama mutanen ne domin 'yan PDP ne sai yace a'a su suna son a basu damar kare kansu ne.Oliseh Metuh yace zasu shiga zaben Bayelsa kuma suna jiran hukuncin kotu akan zaben Kogi.

Wai kamen da ake yi yanzu tamkar bita da kuli ne.

Akan ko INEC zata murde zaben mataimakin daraktan hukumar zaben Nick Dazan ya yi watsi da zargin na PDP. Yace kamata yayi a yi fatali da zargin domin shugaban kasa abun da yake bukata shi ne a yi adalci kuma duk wanda ya ci a bashi.

Haka ma sakataren APC Mai Mala Boni yace kamen da ake yi babu 'yan Bora bare 'yan Mowa, wato babu sabo babu sani, duk wanda ya yi laifi za'a kamashi koshi wanene.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Na Zargin INEC Zat Taimakawa APC Ta Murde Zaben Jihar Bayelsa - 2' 59"