Paralympics: ‘Yar Najeriya Ta Kafa Sabon Tarihi A Gasar Daga Nauyi

Paris 2024 Paralympics - Powerlifting

A ranar Lahadi aka kammala gasar ta Paralympics inda aka yi wasanni wuta a bikin rufe gasar.

‘Yar wasan Najeriya Folashade Oluwafemiayo ta doke tarihin da ta kafa a wasan daga nauyi ta mata a wasannin nakasassu na Paralympics da aka kammala a Paris.

Oluwafemiayo ita take rike da zinaren daga nauyi ajin kilo 86.

Sai ga shi ta shafe wannan tarihi inda ta kafa sabo tarihi wajen daga nauyin kilo 167 a gasar ta nakasassu.

Lokacin da Folashade Oluwafemiayo ta daga nauyin kilo 166, ranar 8 ga watan Satumba, 2024.

Deng Xuemei ta kasar China ce ta lashe kyautar azurfa inda ta daga nauyin kilo 155 sai Nadia Ali ‘yar kasar Masar da ta lashe kyautar tagulla bayan da ta daga nauyin kilo 145.

A ranar Lahadi aka kammala gasar ta Paralympics inda aka yi wasanni wuta a bikin rufe gasar.

Wasan wuta a bikin rufe gasar paralympics a Paris

Nasarar ta Oluwafemiayo na zuwa ne yayin da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya suka samu nasara akan ‘yan wasan Jamhuriyar Benin da ci 3-0 a wasan neman gurbin shiga gasar nahiyar Afirka ta AFCON.