Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Olympics: Biliyan Takwas Aka Kashe wa Tawagar ‘Yan Wasan Najeriya - Minista


Tawagar 'yan wasan Najeriya a lokacin rufe gasar wasannin Olympics a Paris
Tawagar 'yan wasan Najeriya a lokacin rufe gasar wasannin Olympics a Paris

Ma’aikatar za ta kaddamar da cikakken bincike kan dalilin da ya sa Najeriya ba ta tabuka komai ba a wasannin Olympics da aka kammala a Paris, in ji John Enoh.

Ministan wasanni da raya matasa a Najeriya ya ce ma’aikatar za ta kaddamar da cikakken bincike kan dalilin da ya sa Najeriya ba ta tabuka komai ba a wasannin Olympics da aka kammala a Paris, Faransa.

Najeriya ba ta samu kyauta ko daya ba a dukkanin wasannin da ta shiga gasa a Olympics wanda aka kammala a ranar Lahadi.

John Enoh ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis.

A cewar Enoh, za a gabatar masa da rahoto nan ba da jimawa ba.

Ya kara da cewa bai taba tsammanin tawagar ta Najeriya za ta koma gida ba tare da wata kyauta ba.

Enoh ya kara da cewa sama da naira biliyan takwas aka kashewa tawagar da ta wakilci Najeriya a gasar yana mai cewa an biya wasu ‘yan wasa da kudade masu yawa.

Ko da yake, Ministan ya kara da cewa akwai rashin kwarin gwiwa a cikin al’amarin.

Sai dai a karon farko, tawagar 'yan wasan kwallon kwandon ta D'Tigress ta kai zagayen quarter-finals inda ta zamanto kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta kai wannan zagaye a gasra Olympics.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG