Paparoma Francis yayi kira da a dawwamar da zaman lafiya a birnin Kudus, a kuma kawo yarda da juna a yankin kasashen Koriya, a yayin da yake gabatar da jawabinsa na Kirsimeti na bana daga babbar majami'ar St. Peter's dake fadarsa ta Vatican.
A cikin jawabin nasa na bana, wanda ya mayar da hankali a kan ukubar da yara ke sha a rikice rikicen dake faruwa a duniya, Paparoma Francis yayi magana a kqan karuwar tankiya a tsakanin 'yar Isra'ila da Falasdinawa, yana mai fatan cewa aniyar komawa kan teburin shawarwari zata iyaa shawo kan sassan biyu, kuma za'a samu cimma daidaitawar da zata kawo zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu.
A lokacin bukukuwan addu'ar ranar jajiberen Kirsimeti nda ya jagoranta jiya, Paparoman ya kare baki 'yan gudun hijira da babbar murya, har ma yana kwatantasu da yadda Maryamu da Yusuf suka kasa samun wurin zama a Bayt Laham. Yace imani da Allah na nufin cewa tilas a rungumi baki.
Paparoma Francis yayi kira ga kiristoci 'yan darikar katolika su miliyan dubu daya da dari biyu dake fadin duniya da kada su juya bayansu ga 'yan gudun hijirar da aka koresu daga kasashen su a saboda yadda shugabanni ke zub da amincewa da zub da jinin wadenda basu ji ba, ba su kuma gani ba.