Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Bukukuwan Kirsimeti A Baitalami Tun Daga Jiya Lahadi


Bukin Kirsimeti a Baitalami (Bethlehem) na Yamma da Kogin Jordan
Bukin Kirsimeti a Baitalami (Bethlehem) na Yamma da Kogin Jordan

Kamar yadda aka saba duk shekara, jiya an fara bukin kirsimeti a birnin Baitalami (Bethlehem), a yayin da bukin wannan shekarar ya dau salon siyasa saboda ikirarin Isira'ila na mallakar Birnin Kudus da kuma goyon bayan hakan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi.

'Yan kungiyar matasan yara maza na 'boy scouts' da 'yan matan ' girls scouts' da ke yankin Falasdinu sun fara shagulgulan Kirsimeti jiya Lahadi a birnin Baitalami inda su ka yi maci mai burgewa a dandalin Manger Square. Yayin faretin da su ka yi da ya hada da kade-kade da bushe-bushe, sun yi ta wuce wata babbar bishiyar Kirsimeti, wadda aka girke a harabar dadaddiyar majami'ar nan ta wurin da aka haifi Yesu Almasihu.

To amma addini ya garwayu da siyasa sosai a wannan dan karamin garin da ke Yammacin Kogin Jordan, wanda ke karkashin ikon hukumar Falasdinu da duniya ke goyon baya. Don haka wasu manyan alamomi biyu da aka girke a dandalin na Manger Square na dauke na sako mai cewa, "Har abada Birnin Kudus zai cigaba da zama babban birnin Falasdinu."

Wannan shagube ne ga ikirarin Isira'ila na mallakar Birnin Kudus - ikirarin da ya samu goyon bayan Shugaban Amurka Donald Trump makonni uku da su ka gabata - inda Trump ya ce Birnin Kudus "Babban Birnin Isira'ila ne na har'abada."

Batun Birnin Kudus na matukar tasiri a rikicin Isira'ila da Falasdinawa. Ga Isira'ila, nan ne Temple Mount, mai kunshe da manyan Haikaloli biyu na littafin Baibul kuma shi ne wuri mafi tsarki a addinin Yahudu. To amma a yanzu Masallacin Al-Aqsa na wurin, wanda hasali ma shi ne wuri na uku mafi tsari a Islama kuma wani abun alfahari ga Falasdinawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG