Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwa Ta Kashe Mutane Fiye Da 200 A Kasar Filifinu Zuwa Yanzu


Mahaukaciyar guguwa ta janyo ambaliyar ruwa a sassan kasar Filifinu
Mahaukaciyar guguwa ta janyo ambaliyar ruwa a sassan kasar Filifinu

Kamar yadda kasar Filifinu ta saba fuskanta musamman ma a karshen shekara kamar haka, yanzu haka ta na nan ta na fama da mahaukaciyar guguwa, wadda zuwa yanzu ta lakume rayuka sama da 200.

Masu ayyukan ceto na cigaba da neman wadanda ke raya, bayan da wata mahaukaciyar guguwa ta yi kaca-kaca da wasu sassan kasar Philippines a wannan satin, har adadin wadanda su ka mutu ya kusa kai 200.

An dan jinkirta ayyukan ceton bayan da ruwan sama ya cigaba da kwarara kuma gadoji da hanyoyin da ke tsibirin Mindanao au su ka lalace au gocewar kasa ta toshe su sanadiyyar guguwar, mai lakabin 'Tembin.'

Jami'an ayyukan gaggawa sun ce ala tilas mutane sama da 70,000 su ka tsere daga gidajensu a kudancin kasar ta Philippines sanadiyyar mahaukaciyar guguwar.

Kasar ta Philippines kan fuskanci nau'ukan munanan guguwa har 20 kowace shekara, kuma an santa da fama da nau'ukan guguwar a karshen kowace shekara.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG