Paparoma Ya Ayyana Waliyyai Biyu

Paparoma Francis ya ayyana John da John Paul a mastayin waliyyai.
Paparoma Francis, Shugaban 'yan Darikar Katolika, ya ayyana wasu magabatansa biyu - wato John na 23 da John Paul na II - a zaman waliyyai, a wata hidimar da ta gudana yau Lahadi a Dandalin St. Peters da ke birnin Rome.

Jami'ai sun ce wajen mutane miliyan guda ne su ka yi cincirindo a Dandalin St. Peters din da kuma wasu titunan birnin Rome da ke daura da wurin a bikin na ayyana daukaka zuwa waliyanci.

Paparoma Francis ya karanta shelar a hukumance a wurin hidimar daukakawar, wadda ta kuma sami halartar Paparoma murabus Benedict na 16.
Wannan shi ne karo na farko da aka daukaka tsoffin Paparomomi biyu zuwa waliyanci.