Wannan kalamin nasa zai bada kwanciyar hankali ga masu sukar lamirin cewa mai yiyuwa ne kasancewar Paparoman da yayi ritaya a raye zai iya rage kimar sabon Paparoman da zai kama ragamar mulkin cocin ta Katolika ta duniya.
Ana sa ran wannan rana ta yau Alhamis ta kasance ran ace ta hutawa da natsuwa a wurin paparoma Benedict.
Ritayarsa dai zata fara ne daga karfe 8 na marecen yau, agogon Rome.
Daga wannan lokacin ne kofofin fadar Castel Gandolfo zasu rufe kuma daga nan ne dogarawan dake gadinta zasu janye.