Yakin Isra'ila-Hamas: Paparoma Francis Ya Ce A Yi Addu'a, Azumi

Paparoma Francis

A ranar Litinin 7 ga watan Oktoban nan yakin na Isra'ila da Hamas ya cika shekara guda da barkewa.

Paparoma Francis ya yi kiran da a yi addu’a da azumi a ranar 7 ga watan Octoban nan, cikar shekara guda cur da harin da aka kai wa Isra’ila da ya haifar da rikicin da ake yi a Gaza.

A yayin da yawan wadanda ake kashewa da barnar da ake yi ke ci gaba, haka ma kiran wayar da Paparoma ke yi ga mabiya cocin Catholika na Holy Family da ke Gaza ke karuwa, inda yake karfafa gwiwar jagorori da mabiya da ke samun mafaka a cocin.

A farkon fara wata ganawar ibada ta musamman a ranar 2 ga watan Oktoba na malaman Catolika da masu ibada da jagorori a birnin Rome, Paparoma Francis ya yi kiran da a gudanar da addu’oi da azumi a ranar da ake cika shekara guda da soma yaki a Gaza, a yayin da rikicin ke yaduwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Paparoma Francis ya ce, cocin na shirye a ko da yaushe wajen gudanar da aikin al’umma, musamman a wannan lokaci mai abin al’ajabi a tarihinmu, inda iskar yaki ke kadawa, wutar tashin hankali na ci gaba da tartsatsi da neman cinye mutane da kasashe.

Jagoran addinin ya bukaci kowa da kowa da ya shiga wannan addu’a da azumi na kwana guda, domin neman zaman lafiya ga duniya, a ranar 7 ga watan Oktoba.